IQNA

Za A Bayar Da Kyutar Yuro Dubu Uku A Gasar Nisf Sha'aban

Bangaren fasaha: Za a gudanar da gasar Nisf Sha'aban a karo na biyu, inda za a bayar da kyautar kudi yuro dubu uku ga wadanda suka lashe gasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga sashen yada labarai na kwamitin gudanar da gasar Nisf Sha'aban cewa; kamar yadda aka gudanar da gasar Nisf Sha'aban a shekarar da ta gabata a karon farko, a wannan shekara ma za a gudanar da wannan gasa a karo na biyu, inda za a bayar da kudi har yuro dubu uku ga duk wanda ya yi nasara a gasar. A cikin gasar ana bukatar gabatar da wani abu wanda ke nuni ga gwagwarmayar musulunci a wannan zamani, daga cikin abubuwan kuwa hard a makaloli, rahoto na sauti, gajeren fim, hoto. Daga cikin abubuwan da ake son a mayar da hankali kansu kuwa har da batun mai tseratarwa, gwagwarmayar musulunci da kuma makomar duniya, jagoranci da gwagwarmaya daga waki'ar ashura har yau, gwagwarmayar musulunci a duniya, yunkurin bata surar gwagwarmayar musulunci daga kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai, da kuma yahudawan sahyuniya gami da wahabiyawa.

387482