IQNA

An Fassara Kur'ani Da Harshen Turkanci Na Istanbul

16:17 - April 14, 2009
Lambar Labari: 1764955
Bangaren adabi: An fassara kur'ani da harshen Turkanci na Istanbul, wanda cibiyar kula da tarjamar kur'ani da yarukan kasashen waje ta dauke nauyin tarjamawa, kuma daga nan zuwa makonni biyu za a fara sayar da shi a cibiyar sayar da littafai ta Kausar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an fassara kur'ani da harshen Turkanci na Istanbul, wanda cibiyar kula da tarjamar kur'ani da yarukan kasashen waje ta dauke nauyin tarjamawa, kuma daga nan zuwa makonni biyu za a fara sayar da shi a cibiyar sayar da littafai ta (Al-kausar) kuma yanzu haka an tanadi kwafi-kwafi da dama wadanda za a kawo su a kasuwar baje kolin littfai da za a gudanar a birnin Tehran. Shugaban cibiyar kula da tarjamar kur'ani zuwa yaren kasashen waje a Iran Muhammahd Nafadi, ya bayyana cewa cibiyar sayar da littafai ta Kausar da ke kasar Turkiya ita ce ta dauki nauyin yada wannan kur'ani ta hanayar sayar da shi a shagunanta da ke kasar Turkiya da ma wajen kasar. Ya ce a wajen aiwatar da tarjamar, an yi amfani da salo day a yi daidai da abin da sunna da shi'a suka hadu kansa ba tare da wani banbanci ba wajen bayyana ma'anar ayoyi .

387558


captcha