IQNA

Ana Gudanar Da Taro Kan Halayyar Dan Adam A Mahangar Kur'ani

16:16 - April 14, 2009
Lambar Labari: 1764958
Bangaren fikra da ilimi: A taron da ake gudanarwa a kasar Tunusia kan mahangar kur'ani da addinin musulunci kan halayyar dan adam, marubucin nan na kasar Iran Sayyid Muhammad Ismati ya gabatar da makalarsa mai taken sanin halayyar mutane a musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a ci gaba da gudanar da taron da ake yi a kasar Tunusia kan mahangar kur'ani da addinin musulunci kan halayyar dan adam, marubucin nan na kasar Iran Sayyid Muhammad Ismati ya gabatar da makalarsa mai taken sanin halayyar mutane a musulunci.A cikin makalar tasa marubucin Sayyid Muhammad Ismati, ya yi kokarin kawo mahangar musulunci dangane da halayyar dan adam ta hanyar kafa dalilai da ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da bin diddiginsu wajen kawo dalilan safkarsu da nufin tabbatar da dalilinsa kan wannan mahanga. Hakan nan kuma marubucin wanda ya rubuta makalar tasa a cikin harshen larabci, ya yi amfani da salon bayyana ma'anar kalmomi wajen tabbatar da mahangarsa, lamarin da ya samu karbuwa a wajen mahalrta taron.

387167



captcha