Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Wannan rubutun kur'ani da aka samu da kuma ake danganata shi da Imam Musa Kazim (AS) wanda yanzu haka ake ci gaba da ajiye shi a hubbaren Imam Ali Rida (AS) ya fara daga aya 252 a cikin suratul bakara zuwa aya ta 89 a cikin surat Al-imran, haka nan kuma kur'anin ya kunshi shafuka 83, wanda kuma an rubuta shi ne a kan fatar barewa mai launin baki-baki da ke karkata zuwa ga kasa-kasa. Bayanin ya ce tun a cikin shekata ta 1297 shamsiyya wannan kur'ani yake ajiye a cikin dakin karatu na Khusru, amma daga baya ne masana kan kufan tarihi suka gudanar da bincike kansa domin sanin asalinsa, inda daga karshe bayan bin diddigin tarihi suka gano cewa yana da nasaba da Imam Musa kazim (AS)
387460