Bangaren zamantakewa: Shugaban kasar iran zai halarci taron Hadarat Ali Akbar (AS) da za a gudanar a dakin taro na kasa da kasa na gidan radio da talbijin na Iran.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa: wannan taro za a gudanar da shi ne da zummar girmama matasa da suka fi kwazo da fice a gurare na gwamnati da masu zaman kansu da bankoki da kafafen watsa labarai.A wannan taro an kaso matasa gida sha daya a fannonin ilimi da jami'a,bangaren al'adu da fasaha,cibiyoyin kula da iyali ayyukan zamantakewa da hauza da ma'aikatu.Har ila yau akwai bangarori da dama kamar sojoji sa kai,manoma,ma'aikatar kwadago ,wasanni ,kiwon lafiya,masallatai,kungiyoyin agaji,yan jarida,cibiyoyin da ofishin jagora da sauransu.
388337