Ayatullah Jawad Amuli Ya bayyana cewa: Said Muhsin Musawi ya rubuta littafi kan yanayi a musulunci da aka fassara a cikin yarukan farisanci,Larabci da Turanci.
Shi dai wannan littafi ya kumshi yanayin lokutta biyar a cikin shekara kuma wannan littafi ya kumshi nazariya da kuma a aikace kan yanayi a ilimi na tajruba da dabi'a inda a cikin ya yi bayani dalla-dalla kan dan adam zai yi rayuwa cikin sauki tare da kare muhallin da yak e rayuwa ba tare da ya gurbata shi ba .Wannan littafi yanada shafi 344 da kuma aka buga dubu uku a matakin farko. Kuma da Turanci sunansa Islam and Environment.
388239