IQNA

An Fara Rijistar Sunayen Wadanda Za Su Samu Horon Hardar kur'ani A Palastine

14:47 - April 15, 2009
Lambar Labari: 1765412
Bangaren kasa da kasa: An fara rijistar sunayen wadanda za su samu horo kan hardar kur'ani a zirin Gaza, da aka yi take da Tajul wikar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (ma'a) na Palastinu cewa; an fara rijistar sunayen wadanda za su samu horo kan hardar kur'ani a zirin Gaza, da aka yi take da Tajul wikar.Rahoton ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo uku da ake gudanar da irin bayar da horo ga dubban palastinawa matasa a sansanin Rafah, inda shekaru uku kenan a jeer ana bayar da irin wanna horo na tsawon wata biyu a lokutan bazaar, inda matasa da shekarunsu suka haura 12 suke halarta domin hardar kur'ani mai tsarki. Cibiyar kula da harkokin kur'ani da ke gaza ita ce ke daukar nauyin bayar da wannan horo. A cikin ayyukan da cibiyar take gudanarwa na bayar da horon hardar kur'ani mai tsarki, yanzu haka dai ta samara da mahardata da dama tsakanin matasan Gaza.

388224
captcha