IQNA

An Tattauna Batun Shishigin Da Yahudawa Ke Yi Kan Masallacin Qods

14:45 - April 15, 2009
Lambar Labari: 1765414
Bangaren kasa da kasa: Sakataren kungiyar yada ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO Abdulaziz Usman Al-tuwaijari, tare da sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Amr Musa, sun tattauna batun shishigin da yahudawa ke yi kan masallacin Qods.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kungiyar ISESCO cewa; a wata zantawa da ta hada Sakataren kungiyar yada ilimi da al'adun musulunci Abdulaziz Usman Al-tuwaijari, tare da sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Amr Musa, sun tattauna batun shishigin da yahudawa ke yi kan masallacin Qods. Bayanin ya ci gaba da cewa bangarorin biyu sun tattauna kan hanyoyin day a kamata kasashen musulmi da larabawa ya kamata su bi, tare da daukar matakai da suka dace wajen takawa Isra'ila birki kan ta'asar da take tafkawa kan masallacin Qods a kokarin da yahudawa suke na mayar da birnin mallakinsu, tare da hankoron rushe masallacin mai alfarma domin kowa ya rasa. Tun a cikin shekara 1967 ne yahudawan sahyuniya suka mamaye birnin Qods, tare da mayar da dukkanin alamun musulunci da ke birnin zuwa alamu na yahudanci.

388071

captcha