IQNA

Kungiyar Larabawa Nakasassu Ta Bukaci A Duba Halin Nakasassu A Gaza

Bangaren kasa da kasa: Kungiyar larabawa nakasassu ta bukaci gudanar da bincike kan halin da nakasassu da marassa lafiya suke ciki Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (sana) cewa; kungiyar larabawa nakasassu ta sanar da kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ke da mazauni a birnin Alkahira na kasar Masar cewa, tana da dalilai da ta tara kan halin da nakasassu suke ciki, a kan haka suna da bukatar su gudanar da aiki tare da kwamitin bincike kan ayyukan yaki da Isra'ila ta aikata kan al'ummar Gaza, domin hada dukkanin rahotannin baki daya, domin mika su ga kwamitin kare hakkin biladama na majalisar dinkin duniya. Bayanin kungiyar ya ce Isra'ila ta aikata laifukan yaki a kan al'ummar Gaza, inda yanzu haka dubban mutane da suka hada da kanan yara da mata suka zama nakasassu, wasu kuma suka zama marayu. Bayanin ya ce dole a gudanar da bincike kan hakan domin gurfanar da Isra'ila gaban kotun manyan laifuka ta duniya kan laifukan yakin da ta aikata kan al'ummar Gaza.

388198