IQNA

An Bullo Da Wani Sabon Salon Cin Zarafin Musulunci A Tunisia

14:44 - April 15, 2009
Lambar Labari: 1765418
Bangaren kasa da kasa: Wasu mutane da ke cikin wani gungun masu kiyayya da addinin musulunci a kasar Tunisia sun bullo da wata sabuwar hanya ta yin dirar mikiya kan addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet mallakin jaridar (sabq) cewa; mutane da ke cikin wani gungun masu kiyayya da addinin musulunci a kasar Tunisia sun bullo da wata sabuwar hanya ta yin dirar mikiya kan addinin musulunci. Rahoton ya ce mutanen suna yin amfanin da shafin nan na internet da ake tattaunawa a cikinsa tsakanin mutane masu mabanbantan ra'ayoyi domin kare kai da tabbatar da dalilai gami da kwararan hujjoji domin kare ra'ayi, inda wadannan mutane wadanda dukkaninsu 'yan kasar tunisia ne suka shiga cikin wannan tattaunawa domin bayyana ra'ayoyinsu na kin amincewa da addinin musulunci tare da sukar manufofinsa. Rahoton ya ce bayanan da mutanen suke yi a cikin wannan shafin internet ba bayyana ra'ayi ban e kawai, a a hakan cin zarafin addini ne, tare da yin tozarci ga tsarkakan abubuwa da ke cikin addinin musulunci.

388165
captcha