Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran (Quran conferece) cewa; za a gudanar da wani taro kan kur'ani a mahangar tarihi a jami'ar Natradam da ke jahar India a kasar Amurka. Bayanin ya ci gaba da cewa za fara gudanar da taron ne tare da bude shi da lacca daga malamin tarihin nan na kasar Amurka John Jencnez, kuma shugaban jami'ar Natradam da ke cikin jahar Indiana, daga bisani kuma Nasr Abu Hamis zai gabatar da jawabansa. Daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankalin kansu akwai batun rubutun kur'ani, da kuma madogarar tarihi kan kur'ani, da kuma yaren kur'ani gami da adabinsa, inda malaman jami'a gami da masana daga sassa dababn-daban na Amurka za su bayyana ra'ayoyinsu a laccoci ko makalolin da za su gabatar.
385751