IQNA

An Kawo Karshen Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki A Emarat

14:59 - April 15, 2009
Lambar Labari: 1765439
Bangaren kasa da kasa: An kawo karshen bangaren na farko a gasar hardar kur'ani mai tsarki da aka gabatar a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (wam) na kasar Emarat cewa; An kawo karshen bangaren na farko a gasar hardar kur'ani mai tsarki da aka gabatar a Hadaddiyar Daular Larabawa. Rahoton ya ci gaba da cewa wadanda suka shiga cikin gasar matasa ne da shekarunsu ba su wuce tsakanin takwas zuwa zuwa ashirin da daya ba, adadinsu kuma baki daya su 90 ne. Shugaban cibiyar kula da gasar kur'ani ta kasar Emarat ya bayyana cewa, za a zabi wasu daga cikin wadanda suka shiga gasar domin wakiltar kasar a gasar kur'ani ta duniya da za a gudanar nan a wannan shekara.
388078
captcha