IQNA

Yahudawa 'Yan Kaka-Giga Sun Kutsa Kai Cikin Masallacin Qods

Bangaren kasa da kasa: Kimanin yahudawan sahyuniya 'yan kaka-gida dari da talatin ne suka kutsa kai a cikin masallacin Qods mai alfarma inda 'yan sandan Haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kayan sarki ke mara musu baya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Palastinu cewa; A yammacin jiya kimanin yahudawan sahyuniya 'yan kaka-gida dari da talatin ne suka kutsa kai a cikin masallacin Qods mai alfarma inda 'yan sandan Haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kayan sarki ke mara musu baya. Rahoton ya kara da cewa tun a kwanakin da suka gabata ne yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi suka fara barazanar kai hari a kan masallacin Qods tare da hana musulmi gudanar da ayyukan ibada a cikinsa, inda kungiyoyin kare hakkin biladam na duniya suka bayyana daukar duk wani mataki da mai kama da haka da cewa neman tsokanar al'ummar musulmi ne. Bayan da yahudawan masu tsattsauran ra'ayi suka kai harin a jiya, sunkame wani musulmi a lokacin da yake gudanar da salla a cikin masallacin, inda suka yi awn gaba da shi, wanda har zuwa yau ba a san makmarsa ba.

388106