IQNA

Za A Ci Gaba Da Tattauanawar Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Palastinu

22:19 - April 16, 2009
Lambar Labari: 1765727
Bangaren kasa da kasa: Wani daya daga cikin jagororin kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ya bayyana cewa, nan bad a jimawa ba za a ci gaba da gudanar da tattaunawa tsakanin Hamas din da kungiyar Fatah a birnin Alkahira na kasar Masar dangane da batun kafa gwamnatin hadin kan kasa a palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar arabnews cewa; Sami Abu Zuhri daya daga cikin jagororin kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ya bayyana cewa, nan bad a jimawa ba za a ci gaba da gudanar da tattaunawa tsakanin Hamas din da kungiyar Fatah a birnin Alkahira na kasar Masar dangane da batun kafa gwamnatin hadin kan kasa a palastinu. Sami Abu Zuhri ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Gaza. Y ace muna fatan Fatah ta sake dawowa domin ci gaba da wannan tattaunawa da kyakkyawar niya, tare da dakatar da kame mambobin Hamas da take yi a yankunan gabar yamma da kogin Jordan.



389040


captcha