Bangaren kasa da kasa: Babban sakataren ma'aikatar kula da harkokin addin ta kasar Kuwait ya bayyana cewa , ma'aikatarsa t agama kammala dukkanin shirye-shirye domin gudanar da gasar hardar kur'ani da kuma ka'idojin karatunsa Tajwid a karo na goma sha uku a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (al-rayi) da ake bugawa a kasar Kuwait cewa; babban sakataren ma'aikatar kula da harkokin addin ta kasar Kuwait Muhammad Abdulgafar Sharif ya bayyana cewa , ma'aikatarsa t agama kammala dukkanin shirye-shirye domin gudanar da gasar hardar kur'ani da kuma ka'idojin karatunsa Tajwid a karo na goma sha uku a kasar. Sharif ya bayyana hakan ne a gaban wani taron manema labarai da aka gudanar kan batun gasar kur'ani ta kasa, ya ci gaba da cewa gasar za ta hada bangaren hardar kur'ani da kuma ka'idojin karatunsa tajwid, haka nan kuma wadanda za su shiga gasar za su hada matasa masu mabanbantan shekaru. Ya kara da cewa babbar manufar gudanar da irin wannan gasa ita ce karfafa gwiwar matasa wajen karatun kur'ani da hardarsa da sanin ma'anoninsa.
388808