Bangaren adabi: An Gudanar da wani taro domin yin nazari kan tasirin rubuce-rubucen mawakin nan na Iran Sa'adi, kan aladun Iraniyawa gami da adabinsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto bangaren hulda da jama'a na bangaren da ke kula da gudanar da taruka kan makon Sa'adi cewa; an Gudanar da wani taro domin yin nazari kan tasirin rubuce-rubucen mawakin nan na Iran Sa'adi, kan aladun Iraniyawa gami da adabinsu.Wadanda suka gudanar da nazarin kuwa sun hada da masana Iraniyawa da kuma wasu 'yan kasashen waje dangane da rubuce-rubucen da Sa'adi, gami da tarisinsu a cikin al'adun Iraniyawa da kuma duniyar musulmi baki daya. An bayyana sakamakon wannan nazari ne a lokacin da ake gudanar da tarukan makon sa'adi a Iran. Masanan sun yi bayanai masu gamsarwa kan mahangarsa dangane da lamurra da dama da suka shafi ilimi da al'adu, daga karshe kuma an bayar da kyaututtuka ga masanan da suka gudanar da nazarin.
389130