IQNA

An Kore Wata dalibar Jami'a A Faransa Saboda Saka Hijabi

15:49 - April 20, 2009
Lambar Labari: 1766514
Bangaren kasa da kasa: An kori wata dalibar jami'a musulma da ke karatun digirin digirgir a jmai'r Toloz ta kasar Faransa saboda saka hijabin Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Rue cewa; mahukuntan jami'ar Toloz a kasar Faransa sun yanke shawar korar wata daliba musulma mai karatu a wannan jami'ar, inda take a mataki na karshe a karatunta na digirin digirgir, sakamakon yin riko da saka hijabin Musulunci da take a cikin jami'ar, inda yanzu haka kimanin watanni biyu kenan an hana ta gudanar da binciken da take a jami'ar. Dalibar mai suna Poul-Sabatier ta fara saka cikaken hijabin Musulunci ne tun a cikin shekara ta 2006, lamarin da ke bakantawa mahukuntan jami'ar. A nasa bangaren lauya mai kare dalibar ya bayyana cewa dalibar ba ta yi wani abu da ya sabawa ko daya daga cikin ka'idoji da dokokin jami'ar ba, a kan haka zai dauki dukkanin matakai na shari'a domin kare hakkokinta.

389985
captcha