A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da daya daga cikin masana a kasar Labanan Muhammad As'ad, ya bayyana cewa marigayi Imam Khomeini ya kawo wa duniyar musulmi gagarumin canji a cikin duikkanin lamurransu na siyasa da ma na zamntakewa, da dai sauransu. Ya ce tunanin Imam bai takaita da lamurra na siyasa ba, domin kuwa ya baiwa duniyar musulmi wata hanya da za su iya kyautata lamurransu na zamantakewa, musamman ma yadda duniyar musulmi ke fuskantar barazanar shigar bakin al'adu da tunani daga wasu bangarori na waje, da hakan ya hada da gurbacewar al'adun matasa musulmi tare da yin koyi da al'adun yammacin turai. Masanin ya ce Imam ya koyar da duniyar musulmi cewa yin riko da al'adun Musulunci shi ne wayewa. A bangare guda kuma ya wayar da kan musulmi dangane da rashin daidaita lamurran tattalin arziki, ta yadda ba za a samu tazara mai yawa tsakanin masu kudi da talakawa ba.
390002