IQNA

Taron Nuna Yan Uwantaka Ga Al'ummar Palasdinu A Kasar Suriya

Bangaren kasa da kasa: Hukumar tunawa da birnin kudus mai girma a matsayinta na babban birnin al'adu a wannan shekara ta 2009 ta shirya taron tunawa da al'ummar palasdinu.
Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Sana cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: wannan taro a shirya shi ne da zummar tunawa day an uwanmu al'ummar Palasdinu da ke cikin wani mawuyacin hali na kuntatawar da gwamnatin harmtacciyar kasar Isra'ila ke nuna masu a tsawon sheakaru masu yawa ba tare da kib-kibtawa ba .Wannan ba shi ne karon farko da ake kudanar da irin wannan taro a kasar ta Suriya da sauran kasashen lrabawa da na musulmi domin tunawa da halin da al'ummar palasdinu ke ciki.

389617