Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Haveeru) cewa; ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar Maldev ta sanar da kafa wani kwamiti, da zai kula da gyaran tarjamar kur'ani a kasar. Ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar shi ne ya sanar da hakan a jiya alokacin yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro da ma'aikatar ta shirya gudanarwa kan harkokin addini da karatun kur'ani gami da tarjamarsa. Ya ce akwai kur'anai da aka buga da suke dauke da kurakurai wajen tarjamarsu, wanda kuma hakki ne da ya rataya kan ma'aikatarsa da ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen magance wannan matsala, ya ce mataki na farko da suka dauka yanzu shi ne kafa kwamiti da zai kula da dukkanin tarjamar kur'ani da ake yi a kasar, tare da gyara duk wasu kurakurai da aka gani a cikin tarjamar.
389958