IQNA

Jami'oin Kasashen Musulmi Za Su Halarci Taron Jami'oi Na Duniya

16:06 - April 18, 2009
Lambar Labari: 1766527
Bangaren kasa da kasa: Kungiyar jami'o'in kasashen musulmi ta sanar cewa za ta halarci taron jami'o'i na duniya da za a gudanar a kasar Mexico a cikin makon nan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar kula da yada ilimi da al'adun Musulunci ta ISESCO cewa; kungiyar jami'o'in kasashen musulmi ta sanar cewa za ta halarci taron jami'o'i na duniya da za a gudanar a kasar Mexico a cikin makon nan. Wannan dai shi ne karo na uku da kungiyar hadin kan jami'oi ta duniya AIU za ta gudanar da babban taronta, inda za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin ilimin jami'a a matsayi na kasashe da kuma matsayi na duniya. Jami'oin kasashen musulmi za su halarci zaman taron ne domin gabatar da mahangarsu kan lamurran da suka shafi al'adu da ilimi, domin samun karfafa junatsakaninsu da sauran jami'oi na duniya.


389933
captcha