Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta jiyo kamfanin dillancin labarai na APS cewa wannan kasuwar baje kolin littafai za a gudanar da ita ce da zummar yada addinin musulunci da ilimin addini da kuma zai taimakawa marubuta musulmi da larabawa a wannan kasa da kuma sauran shirye-shirye da ked a dangantaka da wannan kasuwar baje kolin littafai.Ustaz Sheikh Seck limamin masallacin juma'a na Luga daga cikin wadanda suka shirya wannan kasuwar baje kolin littafai ya bayyana cewa; irin wannan kasuwar baje koli za ta taimakawa musulmai da marubuta a ciki da wajen wannan kasa ta Senegal da ke da yawan al'ummar kasar musulmai.
389538