Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran (Detnews) cewa; wasu daga cikin kungiyoyin musulmin kasar Amurka sun bukaci babban alkalin kotun kasar Amurka Irec Helder da ya gudanar da bincike kan karar da musulmin kasar suka gabatar masa kan cin zarafin da suke fuskanta daga FBI hukumar yaki da laifuka ta kasar. Kungiyoyin musulmin sun bayyana hakan ne a cikin wata wasika da suka aike wa babban alkalin kotun kolin kasar, inda suka sheda masa cewa suna fuskantar shsshigi daga jami'an hukumar FBI da suke zuwa suna bincika masallatai da cibiyoyin musulmai da ke kasar, wanda hakan ya sabawa dukkanin ka'idoji da dokokin kasar. A kan haka suna neman kotu da ta takawa hukumar FBI birki.
389702