Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta jiyo daga jaridar Aliktisadiya al-elaktroniya ta kasar Saudiya cewa: Gart Wildars dan dan majalisa mai tsananin gaba da addinin musulunci ya sake kaddamar da wata fim ta fitini ta biyu da a ciki yake cin mutuncin addinin musulunci kuma duk da cewa an yi ta yi masa kashedin kar ya kuskura ya kaddamar da wannan fim din amma ya yi kunnan uwar shegu da shure duk wani kira da musulmi suka yi masa kan wannan mummunan mataki na san a batanci kan addinin musulunci da kuma takwalar fada a fili.
389535