IQNA

An Kammala Yi Wa Hubbaren Imamain Na Shi'a A Samra Kwaskwarima

Bangaren manema labarai: Jalal Bitarafan shugaban komitin yiwa Hubbaren Imamain (AS) ya bayyana cewa an kammala yiwa Hubbaren Imamain Na Shi'a a garin Samra Kwakwarima.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa: bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta hubbarin a wannan bukin za a samu halartar manyan malummai da masu kula da sha'anin addini yan Shi'a da Sunna na Iraki da kuma masu kula da Hubbarin Imam Huseini (AS) da Hazarat Abbas (AS) da kuma wasu gungu na yan majalisar dokoki na iraki da za su halarci wannan buki na kaddamar da wannan canji mai albarka matuka gaya.

390096