IQNA

Dogaro Da Kai Shi Ne Babban Abin Da Tsarin Musulunci A Iran Ya Bawa Muhimmanci

17:56 - April 19, 2009
Lambar Labari: 1766982
Bangaren siyasa; Dogaro da kai ta fuskar aikin soji shi ne babban abin da tsarin musulunci yafi maida hankali a kai da hakan zai taimaka al'umma su ji cewa akwai tsaro.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran ce ta watsa rahoton cewa: Ayatullahi Said Muhammad Ali Musawi Jaza'iri wakilin Jagora a lardin Khuzistan a cikin hudubar sallar juma'a a wannan mako ya jinjina da tunawa da ranar soji da cewa: karfin Iran ta fuskar soji alfano ne ga musulmin duniya ya yi da yake hadari ne ga makiyansu.Ya kara da cewa; duk wani nauyi makami da karfi da Iran take da shi a yau babban ci gaba ne ga duniyar musulmi da kuma ya karawa musulmi daukaka da matsayi a yau da kuma nan gaba .Kuma ya tabbatar da raunin da makiyan musulmi da kasashensu ke fuskanta na tunkarar ci gaban da musulmi ke samu a yau .

390079

captcha