Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa: wannan littafi da aka tarjama a cikin harshen Rashanci ya kumshi rayuwar Annabi Musa (AS) daga ranar haifuwarsa har zuwa karshen aikin da aka aiko shi zuwa al'ummarsa da kuma irin darussan da ke cikin rayuwarsa da za mu iya yin koyi da shi.A wani bangare na littafin an yi bayani kan yadda ya samu Allah Ya kubutar da shi daga hannun azzalumi Fir'auna da yadda ya rayu a fadar Fir'auna da kuma yadda ya yi magana da Allah Madaukakin Sarki da sauran abubuwa na shiryarwa.
390098