IQNA

An Watsa Littafin Masihu A Cikin Kur'ani

17:59 - April 19, 2009
Lambar Labari: 1766985
Bangaren Fasaha;An watsa littafin Masihu A Cikin Kur'ani da wani dan jarida dan kasar Bulgariya ya rubuta karkashin taimakon Ayatullahi Kur'ani .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani ce ta watsa labarin cewa: tuni aka kammala bugawa da kuma watsa shi a bainar jama'a littafin nan da wani dan jarida dan kasar Bulgariya ya rubuta kan Masihu A Cikin Kur'ani .Kuma ya rubuta wannan littafi ne saboda wayar da kan al'ummar kasar kan muhimmancin sanin addini da wayewa irin ta addini da kuma yadda musulmi sama da miliyon daya a wannan kasa ke rayuwa da hakan zai taimaka wajen samun kusanci tsakanin musulmai day an uwansu mabiya sauran addinai.

390069

captcha