IQNA

An Watsa Littafin Mahdi Ali Muhammad A Cikin Littafan Sunna

Bangaren al'adu da fasaha: littafin Mahdi Ali Muhammad a cikin Littafan Sunna da Hadi Amiri Ya rubuta an watsa shi.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani ce a Iran Ikna ta watsa labarin cewa; littafin da ke bayani kan hujjojin tabbatar Imam Mahdi a cikin litattafan Ahlul Sunna da Hadi Amiri ya rubuta tuni ya shiga kasuwa da kuma ya samu karbuwa ta musamman.Har ila yau a cikin wannan littafi an yi bayani dalla-dalla tare da hujjoji kan bayyanar Immam mahdi (AF) da kuma a cikin maganganu da litattafan manyan malumman Sunna kuma littafin ya kumshi shafi 400 da ake sayar da shi kan farashi dubu hudu da dari biyar na tuman kudin Iraniyawa.

390054