Bangaren kasa da kasa: Kwamitin kasashen larabawan tekun fasha ya yi Allawadai da ayyukan cin zalun da Isra'ila ke aikatawa kan palastinawa, da kuma ayyukan wuce da irin da take kan masallacin Qods mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria cewa; Kwamitin kasashen larabawan tekun fasha ya yi Allawadai da ayyukan cin zalun da Isra'ila ke aikatawa kan palastinawa, da kuma ayyukan wuce da irin da take kan masallacin Qods mai alfarma. Kwamitin kasashen larabawan tekun fashan ya sanar da hakan ne a cikin wani bayani day a fitar yau, inda ya bayyana cewa dukkanin ayyukan zalunci dad a Isra'ila take aikatawa kan palastinawa musamman ma mazauna birnin Qods, yunkuri ne na rusa masallacin Qods mai alfarma da yahudawan sahyuniya ke yi domin kowa ya rasa. Bayanin ya kara da cewa ci gaba da aikata wadannan munan ayyuka da yahudawan sahyuniya ke yi kan al'ummar musulmin palastinu ba shi ne zai bas u zaman lafiya ba, kuma dole ne gwamnatin yahudawan ta kawo karshen hakan cikin gaggawa.
390497