IQNA

ISESCO Ta Yi Allawadai Da Gina Ramuka A Masallacin Qods Da Isra'ila Ke Yi

17:58 - April 19, 2009
Lambar Labari: 1766997
Bangaren kasa da kasa: A wani zama da kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO ta gudanar a daren jiya kan kufan tarihin musulunci, ta yi Allawadai da matakan da Isra'ila ke dauka na wuce gonad a iri wajen cin zarafin al'ummar palastinu, da kuma gina ramuka a cikin masallacin Qods mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Al-dastur da ake bugawa a kasar Jordan cewa; a wani zama da kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO ta gudanar a daren jiya kan kufan tarihin musulunci, ta yi Allawadai da matakan da Isra'ila ke dauka na wuce gonad a iri wajen cin zarafin al'ummar palastinu, da kuma gina ramuka a cikin masallacin Qods mai alfarma. Zaman wanda aka gudanar a birnin Aman na kasar Jordan ya samu halartar masana musulmi daga kasashe daban-daban, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tarihin musulunci a ilmance, haka nan kuma sun tabo batun halin da al'ummar palastinu suke ciki, inda suke fuskantar zalunci da danniya daga yahudawan sahyuniya, da kuma yunkurin da yahudawan sahyuniya ke na rushe masallacin Qods, mahalarta taron sun yi Allawadai da wannan mataki na tsokana.


390447
captcha