IQNA

Za A Gudanar Da Taron Tattalin Arziki Na Kasashen Musulmi A Malazia

17:58 - April 19, 2009
Lambar Labari: 1766998
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da taron bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi mabobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a kasar Malazia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Tradehakra cewa; za a gudanar da taron bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi mabobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a kasar Malazia. Bayanin ya kara da cewa babbar manufar gudanar da wannan taron dai ita ce samar da hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasashen musulmi, musamman ma bisa la'akari da matsalar tattalin arziki da kasashen duniya ke fuskanta a cikin wannan lokaci. Wanna dai shi ne karo na takwas da kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC suke gudanar da zama domin tattauna batutuwa da suka shafi harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi.

390085
captcha