IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Fikirar Addini A Zamanin Yau

Bangaren fikira: Za a gudanar da taro kan fikirar addini a zaman yau a karo na biyu a hamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda za a gudanar a cikin jami'o'in kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; za a gudanar da wannan taron ne a jami'ar shahid Beheshti da ke birnin Tehran, da nufin yada tunani da mahangar addinin Musulunci a a tsakanin daliban jami'a. A cikin wata zantawa da ta hada banagaren kula da hulda da jama'a a na jami'ar Shahid Beheshti da ke birnin Tehran da kuma wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Uzma Sayyid ali Khamenei, Sayyid Ali sayyid Abu Talib, ya bayyana cewa za a gudnar da taron ne tare da halartar masana da malaman jami'o'i gami da malaman addini, tare da halartar dalibai daga jami'oi daban-daban na Iran da kuma dalibai daga cibiyar ilimin addinin Musulunci ta Hauza da ke Qom da ma sauran rassanta da ke cikin Iran, inda za a gabatar da jawabai ga mahalarta taron, tare da raba makaloli kan abubuwan da taron zai yi dubi kansu.


390151