Kamfanin dillancin labaran Ikna a reshen Labanan ya habarta cewa; An gudanar da wani taro na musamman a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanan domin nuna goyon baya ga Qods dangane da barazanar da masallacin Qods da ma al'ummar birnin ke fuskanta daga yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi. Rahoton ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar ,asana daga sassa daban-daban na kasar Labanan da ma wasu kasashen larabawa, inda suka jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ke fuskantar baraza daga yahudawan sahyuniya, tare da yin Allawadai da matakin da yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ke nufin dauka na rushe masallacin Qods, taro ya nuna goyon baya ga Qods, tare da bayyana shiri na kare masallacin daga duk wata barazanar yahudawan sahyuniya.
390128