Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; limamin juma'a a birnin Ganabad ya bayyana cewa; Iran za ta koya wa Isra'ila babban darasi, matukar dai ta kai harin soji a cikin kasarta. Hojjatol Islam Hassan Sadeghi ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake gabatar da hudubar juma'a a wannan mako, ya ci gaba da cewa har kullum Iran tana son zaman lafiya ne da kowa, kuma ba ta da nufin kai hari akan wata kasa ko wata al'umma, amma kuma hakan ba ya nufin cewa wata kasa za ta taba ta ta kwana lafiya. Ya ce a cikin 'yan lokutannan Haramtacciyar Kasar Isra'ila na ci gaba da yin barazanar kai hari a kan tashoshin nukiliyar Iran, bisa zaton cewa za ta sha lalai, ya ce idan har gwamnatin yahudawan ta yi wannan kuskure to kuwa za ta koyi babban darasi daga Iran.
390181