IQNA

Juyin Musulunci A Iran Ya Ginu Ne Kan Koyarwar Kur'ani

17:27 - April 19, 2009
Lambar Labari: 1767010
Bangaren fasaha: Ayyukan sinima kan juyin juya halin Musulunci ko alama ba su fita daga koyarwar kur'ani ba, domin kuwa juyin juya halin da aka yi a Iran ya ginu ne tare da dogara a kan koyarwa irin ta kur'ani mai tsarki.
A cikin wata zantawa da ta hada dan wasan sinima na kasar Iran Mas'ud Rassam da kuma kamfanin dillancin labaran Ikna ya bayyana cewa; ayyukan sinima kan juyin juya halin Musulunci ko alama ba su fita daga koyarwar kur'ani ba, domin kuwa juyin juya halin da aka yi a Iran ya ginu ne tare da dogara a kan koyarwa irin ta kur'ani mai tsarki. Ya ci gaba da cewa babbar manufar ayyukan sinima da ake gudanarwa a Iran ita ce wayar da kan al'umma dangane da zamantakewa daidai da koyarwa irin ta Musulunci, kamar yadda fina-finan da aka shirya kan siyasa su ma suna kiyaye ka'idoji da kuma darussa da ya kamata al'umma ta dauka ta wannan fuska, dangane da fina-finai da ake shirya kan juyin juya hali kuwa, suna bayyana hakikanin abin da ya faru ne a lokacin juyin, da kuma ilmantar da wadanda ba su san hakikanin abin da ya faru ba, sakmakon bayanai na kuskure da ake ba su kan hakan.

390075
captcha