IQNA

Yin Tattali Da Hana almubazziranci Zai Taimaka Wa Hukuma

Bangaren siyasa da zamantakewa: tattali da hana almubazziranci bayan siyasa yana taka rawa da tasiri da kuma hana yin kane-kane a dukiyar al'umma.
Hujjatullah Muhammad Ali Kasimi malami a cibiyar ilimi da tarbiya ta Imam Khomeini ® a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa; tattali da hana almubazziranci yana raya al'umma da bada matsayi da girman day a yi daidai da ita kuma yana taimakawa al'umma a wajen samun ci gaba da aiki da nauyin day a rataya a kan ta.Har ila yau yana zama jagora ga masu mulki da jan ragamar al'umma a kullum ta hanyar sara da duba bakin gatari.Duk wata al'umma da bata da tattali da tsumi da tanadi za ta iya fadawa cikin wani hali mawuyaci da fuskantar matsaloli barkatai.



390835