Bangaren Zamantakewa; Hujjatul islam Haj Ali Akbar a yau a lokacin da yke gabatar da jawabin bude taron girmama matasa Iraniyawa da suka taka rawar gain a fadin Iran ya bada labarin kafa sakatariyar dindindin na shirya wannan baje koli na Hadarat Ali Akbar (AS).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta jiyo da hujjatul Islam da musulmi Mahammad Jawad Haj Ali Akbari shugaban hukumar da ke kula day an kasa matasa a safiyar yau a lokacin da yake jawabin bude taron girmama matasa da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban day a taimakawa ci gaban al'ummar Iran inda aka samu halartar shugaban kasar Iran Ahmadi Najad a wannan taro da aka shirya a babban dakin taro na kasa da kasa na gidan radiyo da talbijin na Iran day a jinjinawa matasan da suka zamanto abin koyi da kuma suka yi fice a fadin Iran.
390783