Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na jaridar Al-iqtisadiyya ta kasar Saudiyya cewa; za a kammala gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci jami'an tsaro a kasar Saudiyya a birnin Riyad fadar mulkin kasar. Bayanin ya ce za a gudanar da taron kammala gasar ne a babban dakin taro na ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar saudiyya da ke birnin Riyad, taron da ministan harkokin cikin gidan kasar Saudiyya Amir Nayif Bin Abdiaziz zai jagoranci gabatarwa. Babban daraktan ma'aikatar da ke kula da harkokin addini da shirya gasar kur'ani a kasar saudiyya A'id Karni, ya bayyana cewa manufar gudanar da wannan gasa dai it ace karfafa gwiwar jami'an tsaro, kama daga sojoji har zuwa 'yan sanda wajen mayar da hankali ga karatun kur'ani da kuma hardarsa.
390821