Bangaren kasa da kasa: Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga Isra'ila a birnin Jenneva fadar mulkin kasar Switzerland, kafin fara gudanar da taron kasa da kasa kan wariya da majalisar dinikin duniya ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga Isra'ila a birnin Jenneva fadar mulkin kasar Switzerland, kafin fara gudanar da taron kasa da kasa kan wariya da majalisar dinikin duniya ta shirya. Rahoton ya ce kungiyoyin farar hula na kasar Switzerland da wsu kungiyoyin farar hula na kasashen larabawa da na Afirka ne suka shirya gudanar da wannan jerin gwano, inda suka yi Allawadai da ayyukan nuna wariya da Isra'ila ta aikatawa kan al'ummar palastinu, tare da yin kakkausar suka dangane da yadda take gallaza musu. A yayin gudanar da zaman taron mahalrta za su fitar da bayanai kan wariya da kuma mummunar illa da ke tattare da hakan, daga karshe kuma a cikin bayanin bayan taro za a yi Allawadai da Isra'ila kan kan cin zarafin dan adam da take yi tare da nuna wa al'ummar palastinu wariya.
390727