A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani masani dan kasar Labanan Muhammad sa'ad ya bayyana cewa; dole ne a kirkiro sabbin hanyoyi wajen kara fadada ayyukan kur'ani da wayar da kan matasa musulmi dangane da muhimmancin da ke tattare da yin riko da koyarwa irin ta addinin mulunci. Ya ci gaba da cewa bisa la'akari da canjin zamani ya zama wajibi a yi amfani da sabbin hanyoyi na zamani dab a su saba wa shari'a ba wajen fadada ayyukan da ake gudanarwa kan kur'ani da ilmominsa, da kuma wayar da kan matasa musamman ma 'yan jami'a, dangane sahihin tafraki na koyarwar addini, ta yadda za a kauce wa gurbatar al'adu. Ya ce babu wani dalili da zai sanya a ki yin amfani da sabbin hanyoyi na zamani wajen yada tunanin addinin musulunci tsakanin matasa.
390228