IQNA

An Ware Riyal Biliyan 200 Domin Ayyukan Kur'ani A Iran

16:31 - April 20, 2009
Lambar Labari: 1767589
Bangaren rahoto: Babban daraktan ma'aikatar da ke kula ayyukan kur'ani da masallatai a kasar Iran, ya bayyana cewa a wannan shekarar an ware makudan kudi da suka kai riyal biliyan dari biyu domin gudanar da ayyukan kur'ani da kuma kula da masallatai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Rahim Ja'afari babban daraktan ma'aikatar da ke kula ayyukan kur'ani da masallatai a kasar Iran, ya bayyana cewa a wannan shekarar an ware makudan kudi da suka kai riyal biliyan dari biyu domin gudanar da ayyukan kur'ani da kuma kula da masallatai. Ja'afari ya bayyana hakan ne wajen kaddamar da wani shiri na gina wata cibiyar gasar karatun kur'ani a garin Arumiyeh da ke cikin lardin Azarbaijan. Ya ci gaba da cewa ma'aikatarsa za ta bayar da muhimmanci matuka a wannan shekara wajen fadada ayyukan kur'ani a duk fadin kasar, da kuma shirya gasa a sassa daban dabandaban na kasar domin kara karfafa gwiwar mahardata da kuma makaranta kur'ani wajen mai hankali da himma. Ya ce wannan kuma ita ce babbar manufar gwamnati kan ware makudan kudi domin ayyukan kur'ani a fadin kasar.


390493


captcha