IQNA

Kwanciyar Hankalin Larabawa Na Tattare Ne Da Zaman Lafiya A Palastinu

Bangaren siyasa da zamantakewa: Ministan ma'aikatar kula da ayyuka a kasar Labanan kuma mamba akungiyar gwagwarmaya ta hizbulla Muhammad Finish ya bayyana cewa isar da taimako ga al'ummar palastinu aiki ne na 'yan adamtaka, kuma kwanciyar hankalin al'ummomin larabawa na tattare ne da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wani jawabi day a gabatar jiya a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanan, ministan ma'aikatar kula da ayyuka a kasar Labanan kuma mamba akungiyar gwagwarmaya ta hizbulla Muhammad Finish ya bayyana cewa isar da taimako ga al'ummar palastinu aiki ne na 'yan adamtaka, kuma kwanciyar hankalin al'ummomin larabawa na tattare ne da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a palastinu. Ya ci gaba da cewa idan aike wa al'ummar palastinu da taimako laifi ne to su sun amince da wannan laifin, domin a cewarsa sun amma kan cewa tsaron kasar Labanan da ma sauran kasashen larabawa yana tattare da samun tsaro a palastinu. Ya ci gaba da cewa ko ba komai taimaka ma al'ummar palastinu aiki ne na 'yan adamtaka, domin kuwa mun ga kungiyo na kasashen duniya dab a na musulmi ba ne ko na larabawa suna kai taimako ga al'ummar palastinu.


390762