Bangaren kasa da kasa: Babban daraktan cibiyar kula da harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO Abdulaziz Al-tuwaijari, ya bayyana cewa dukkanin kasashen musulmi suna tare da batun kare masallacin Qods daga shishigin yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Al-watan da ake bugawa a kasar Saudiyya cewa; babban daraktan cibiyar kula da harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO Abdulaziz Al-tuwaijari, ya bayyana cewa dukkanin kasashen musulmi suna tare da batun kare masallacin Qods daga shishigin yahudawan sahyuniya. Al-tuwaijari ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani da cibiyar ta fitar, inda ya jaddada cewa kasashen musulmi za su iya taka muhimmiyar rawa wajen taka wa Isra'ila birki kan munanan manufofinta a kan al'ummar palastinu da kuma masallacin Qods mai alfarma, musamman ma idan a ka yi la'akari da rawar da suke takawa ta fuskacin harkokin tattalin arziki a duniya.
391538