Bangaren kasa da kasa: Shugaban kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan Auglo ya bayyana cewa; bisa la'akari da matsalolin tattalin arziki da suka addabi duniya, kasashe mambobi a kungiyar OIC za su gudanar da wani zaman taro a nan gaba domin fuskantar matsalar tare da samo hanyoyin rage tasirinta a cikin kasashen Musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Qods press cewa; shugaban kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan Auglo ya bayyana cewa; bisa la'akari da matsalolin tattalin arziki da suka addabi duniya, kasashe mambobi a kungiyar OIC za su gudanar da wani zaman taro a nan gaba domin fuskantar matsalar tare da samo hanyoyin rage tasirinta a cikin kasashen Musulmi. Auglo ya bayyana hakan ne a wani zama da kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na kasashen musulmi a karkashin kungiyar OIC ya gudanar. Ya ce ko shakka babu wannan zama za a gudanar zai taimaka wajen samun hanyoyin da suka dace domin magance wannan matsala ko dakushe kaifinta.
391459