Bangare kasa da kasa: Kimanin mutane dari bakwai ne da ke bukatar ganin an gudanar da shari'ar musulunci a kasar Somalia sun gudanar da wani gangami a birnin Magashou fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa cewa; sama da mutane dari bakwai ne da ke bukatar ganin an gudanar da shari'ar musulunci a kasar Somalia sun gudanar da wani gangami a birnin Magashou fadar mulkin kasar. Rahoton ya ci gaba da cewa a lokacin da ake gudanar da gangamin, daruruwan mutane sun daga hotunan sabon shugaban kasar suna cewa sulhu ga Somalia musulunci ga Somalia. Ministan harkokin cikin gida na kasar Somalia Abdulkadir Ali Umar ya bayyana cewa; dukkanin bangarori sun amince da batun gudanar da shari'ar musulunci a kasar Somalia, a kan haka wannan shi ne babban aikin da ke gaban gwamnati a halin yanzu ta yi wa al'umma abin da suke bukata.
391429