Bangaren fasaha: Ministan ma'aikatar kula da al'adu ta Iran ya bayyana cewa, irin ayyukan fasaha na musulunci da ake gudanarwa a Iran wadanda ake yi domin cikin gida da kuma wadanda ake yi domin fitarwa a wajen kasar abin yabawa ne.
Kamfanin dillancin labaran ikan ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na ma'aikatar kula da harkokin al'adu na Iran cewa; Ministan ma'aikatar ya bayyana cewa, irin ayyukan fasaha na musulunci da ake gudanarwa a Iran wadanda ake yi domin cikin gida da kuma wadanda ake yi domin fitarwa a wajen kasar abin yabawa ne. ya ci gaba da cewa irin ayyuka na wasan kwaikwayo da ake shiryawa da gabatarwa a Iran suna da matukan kayatarwa ga dukkanin masom kallo, kuma hakan wata hanya ce da ake yin amfani da ita wajen isar da sakonni da dama ga al'ummar Iran din da ma sauran al'ummomi na duniya, musamman kan harkokin rayuwa ta zamantakewa da kuma ilmantarwa kan wasu abubuwa da suka shafi addini da rayuwa ta yau da kullum. Ya ce ma'aikatarsa za ta ci gaba da yin namijin kokari wajen karfafa harkokin wasan kwikwayo fina-finai da dai sauransu a Iran.
391574