IQNA

Babban Malamin Kasar Afganistan Ya Rasu Sakamakon Harin Bam

Bangaren siyasa da zamantakewa: Babban malamin nan na kasar Afganistan Maulavi Abdulkahir, ya rasa ransa sakamakon kai wani harin bam da sojojin kawance na nato suka kai karkashin jagorancin Amurka a yankin Logar na kasar Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran ikan ya reshen kasar Afganistan ya habarta cewa; babban malamin nan na kasar Afganistan Maulavi Abdulkahir, ya rasa ransa sakamakon kai wani harin bam da sojojin kawance na nato suka kai karkashin jagorancin Amurka a yankin Logar na kasar Afganistan. Rahoton ya ci gaba da cewa jiragen yakin dakarun nato sun rowan bama-bamai a kan yankin Logar da sunan yunkurin murkushe 'yan ta'adda, inda suka saki bama-bamai a kan gidan shehin malamin, wanda al'ummar kasar Afganistan ke girmamawa a loakcin da yake cikin gidansa, lamarin da ya yi sanadiyar yin shahadarsa. Jima kadana bayan yaduwar labarin rasuwarsa sakamakon kai harin na darun nato, shugaban kasar afganistan Hamid karazai ya fito karara ya yi Alladawai da kai harin, tare da yin kira da a gudanar da binciken gaggawa kan hakan, ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan malamin da kuma al'ummar musulmi ta kasar Afganistan.

391048