IQNA

An Yi Allawadai Da Parpagandar Masar A Kan Hizbullah

17:37 - April 21, 2009
Lambar Labari: 1768139
Bangaren siyasa: Sakataren kwamitin kasa da kasa na goyon bayan palastinu ya yi Allawadai da matakan parpaganda da gwamnatin kasar Masar take dauka domin buce hasken kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah.
Kamfanin dillancin labaran Ikan ya habarta cewa; Sakataren kwamitin kasa da kasa na goyon bayan palastinu ya yi Allawadai da matakan parpaganda da gwamnatin kasar Masar take dauka domin buce hasken kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah. Ya ci gaba da cewa babu wani abu na laifi da Hizbullah ta aikata wajen aikewa da taimako ga al'ummar Gaza, amma abin mamaki shi ne yadda gwamnatin Masar din ta yi amfani da wannan dammar wajen yada karairayi dangane da Hizbullah domin kawai ta cimma wasu manufofi da kowa ya san cewa na siyasa ne. ya ci gaba da cewa abin da Hizbullah ta yi nauyi day a hau kan dukkanin wani mutum mai lamiri a duniya ba sai musulmi ba kawai, saboda haka abin kungiyar ta yi ta safke nauyinta ne.

391541



captcha