Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya cewa, cibiyar kula da ayyukan alkhairi ta kasar ta shirya gudanar da wani taro na nishantar da mata da shekarunsu suka kama daga 13 zuwa 30, inda za a yi amfani da wannan dammar wajen wayar da kansu kan ilmomin kur'ani, ta yadda za su yi aiki da su a cikin harkokinsu na rayuwar yau da kullum. A wajen taron za a gudanar da laccoci, tare da wasannin kwaikwayo na nishadantarwa, kuma za a baje kolin wasu daga cikin littafan musulunci da magabata suka rubuta kan muhimmancin rawar da mata suke takawa a cikin harkokin rayuwar al'umma ta zamantakewa.
392944